Luke 21

Bayarwar Gwauruwa

1Da Yesu ya ɗaga ido, sai ya ga waɗansu masu arziki suna sa baikonsu a maʼajiyin haikalin. 2Ya kuma ga wata gwauruwa matalauciya, ta saka anini biyu. 3Sai ya ce, “Gaskiya ina faɗa muku, wacce nan gwauruwa matalauciya ta sa fiye da dukan sauran. 4Dukan mutanen nan sun ba da baikonsu daga cikin arzikinsu ne, amma ita daga cikin talaucinta, ta saka duk abin da take da shi na rayuwa.”

Alamun Ƙarshen Zamani

5Waɗansu daga cikin almajiransa, suka fara magana a kan yadda aka yi wa haikalin ado da duwatsu masu kyau, da kuma kyautai da aka keɓe wa Allah. Amma Yesu ya ce, 6“Wannan abin da kuke ƙallo a nan, lokaci yana zuwa da ba za a bar wani dutse a kan wani dutse ba. Kowanensu, za a rushe shi.”

7Suka tambaye shi suka ce, “Malam, yaushe waɗannan za su faru? Kuma wace alama za ta nuna cewa suna dab da faruwa?”

8Ya amsa ya ce, “Ku lura, kada ku kuma a ruɗe ku. Gama da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ai, ni ne shi,’ da kuma, ‘Lokaci ya yi kusa.’ Kada ku bi su. 9Saʼad da kuka ji labarin yaƙe-yaƙe, da juye juyen mulki, kada ku tsorota. Dole ne waɗannan abubuwa su fara faruwa, amma ƙarshen ba zai zo nan da nan ba.”

10Sai ya ce musu, “Alʼumma za ta tasar wa alʼumma, mulki zai tasar wa mulki. 11Za a yi manyan girgizan ƙasa, da yunwa, da annoba a wurare dabam-dabam, da kuma abubuwa masu bantsoro, da manyan alamu daga sama.

12“Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majamiʼu, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana. 13Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su. 14Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda da za ku kāre kanku. 15Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata. 16Har iyayenku, da ʼyanʼuwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku. 17Duk mutane za su ƙi ku saboda ni. 18Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba. 19Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.

20“In kuka ga mayaƙa sun kewaye Urushalima, za ku sani rushewarta ya yi kusa. 21A lokacin nan, bari waɗanda suke Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. Bari waɗanda suke cikin birnin kuma su fita, bari kuma waɗanda suke ƙauye kada su shiga birnin. 22Gama wannan shi ne lokacin hukunci, saboda a cika duk abin da aka rubuta. 23Zai zama abin kaito ga mata masu ciki, da mata masu renon ʼyaʼya, a waɗancan kwanakin! Za a yi baƙin ciki mai tsanani a ƙasar, da kuma fushi mai tsanani a kan mutanen nan. 24Za a kashe su da takobi, a kuma ɗauke su ʼyan kurkuku, zuwa dukan alʼummai. Alʼummai za su tattaka Urushalima, har sai lokacin Alʼummai ya cika.

25“Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, alʼummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku. 26Mutane za su suma don tsoro, za su kuma yi fargaba, a kan abin da yake zuwa a bisan duniya, gama za a girgiza duniyar taurarin sararin sama. 27A lokacin ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin girgije, da iko, da ɗaukaka mai girma. 28Saʼad da waɗannan abubuwa sun fara faruwa, ku tashi tsaye, ku ɗaga kawunanku, domin fansarku yana matsowa kusa.”

29Sai ya gaya musu wannan misali, ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa. 30A duk lokacin da sun fara fitar da ganye, za ku gani da kanku, ku san cewa, damina ta yi kusa. 31Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya yi kusa.

32“Gaskiya nake gaya muku, ba shakka, wannan zamani ba zai shuɗe ba, sai dukan waɗannan abubuwa sun cika. 33Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba. 34Ku lura fa don kada son annashuwa na banza, da shaye-shaye, da damuwa na rayuwa su rinjayi zuciyarku, har ranar ta auko muku, ba tsammani, kamar tarko. 35Gama za ta zo a kan kowa da yake kan dukan duniya. 36Ku yi tsaro kullum, ku yi adduʼa don ku iya kuɓuta daga dukan waɗannan abubuwa da suke kusan faruwa, don ku iya tsayawa a gaban Ɗan Mutum.”

37Kowace rana, Yesu yakan je haikalin ya yi koyarwa, da kowace yamma kuma, ya je ya kwana a kan tudun da ake kira Dutsen Zaitun. 38Da sassafe kuma, dukan mutanen suka zo haikalin, don su saurare shi.

Copyright information for HauSRK